
Shahararren Shugaban ‘Yan Bindiga Kachalla Dan Lukuti Ya Mutu Cikin Wani Mummunan Yanayi, Yayin Da Yayita Ihu Kamar Kare Har Sai Da Ya Cika…
Shahararren dan fashin nan mai suna Kachalla Dan Lukuti, wanda ya saba jagorantar munanan hare-hare a jihohin Zamfara da Katsina, ya rasu bayan ya sha fama da wata bakuwar rashin lafiya da ta sa shi yin ihu kamar kare kafin rasuwarsa.
Wasu majiyoyi da suka sun shaida Zagazola, kwararren mai sharhi a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi cewa Dan Lukuti ya kamu da rashin lafiya kimanin mako guda da ya gabata, inda ya fara samun alamomin da ba a saba gani ba wadanda suka hada da tashin hankali, rashin kamun kai, kuma daga karshe, ya ci gaba da yin kukan da ke kama da na kare.
Majiyoyin sun ce ’yan kungiyarsa ba su samu damar zuwa wajensa ba, saboda yadda halin da yake ciki ke ciki, lamarin da ya tilasta musu yin nesa da shi har sai da ya mutu.
Dan Lukuti ya kasance shugaban ‘yan bindiga da ake fargaba, yana aiki daga dajin Kokonba da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.
Yana jagorantar ‘yan bindiga sama da 50, kuma shi ne ke da alhakin kai hare-hare da dama a garuruwan Dan Jiloga, Rijiya, Zonai, Magami, da kan babbar hanyar Gusau zuwa Magami, inda ya taba kai hare-hare a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.
Duk da ta’addancin da ya yi, lokacinsa na ƙarshe ya sha wahala da ba za zai iya jurewa ba, kamar yadda shaidun gani da ido suka ruwaito cewa yana kururuwa da kuka har ya mutu.
’Yan kungiyarsa, saboda tsoro da camfe-camfe, sun tilasta wa mutanen kauyen Kizara gudanar da jana’izarsa, inda suka kwantar da shi a makarantar firamare ta yankin.