Shugaban Hukumar tsaftace birni da muhalli (REMASAB) ya kai ziyarar gani da ido babbar kwatar Kwarin Gogau, bayan da ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Fagge, Hon. Barrister Muhammad Bello Shehu ya kai ƙorafi abisa ambaliyar ruwa da kwatar take jawowa.

 Da yake jawabi majalisar tarayya maiwakiltar karamar hukumar fagge ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne duba da kusantowar damuna, da kuma irin asarar dukiya da rayukada al’umma da ake  fama dashi abisa ambaliyar ruwa.

Dan majalisar yasha Alwashin magance matsalar ambaliyar ruwa a yanki Unguwar fagge da kewaye.

Anasa bangaren shugaban hukumar kwashe shara ta jihar kano Lameen Muktar Hassan ya bayyana cewa hukumar kwashe shara ta jihar kano zatayi duk mai yuwuwa  wajen tsaftace jihar kano ta yadda za’a magance  matsalar ambaliyar ruwa a jihar kano