Kimanin dalibai 60 ne suka amfana da tallafin karatu kyauta wanda
Gidauniyar Margayi Kabiru Abubakar karkashin kulawar Dan Majalissar Tarayya Mai Wakiltar Bichi. (Dr.) Abubakar Kabir Abubakar ta dauki nauyi karatun su yan asalin Karamar hukumar Bichi, domin yin karatun aikin jinya a kwalejin horar da ma’aikatan jinya da unguwar zoma ta Flagship dake bichi.

Kwamitin ilimin Dan Majalissar Tarayya karkashin jagorancin Dr. Habibu Usman Bichi, ya jagoranci raba takardar fara karatu (Admission letter) ga wadannan dalibai a Ranar laraba bayan sun samu nasara a tantancewar da akayi musu.

da yake jawabi yayin taron Babban mataimaki ga Dan majalisar Sabo Iliyasu saye ya bayyana cewa gidauniyar ta marigayi Abubakar Kabir bichi zataci gaba da tallafawa alummar Karamar Hukumar ta bichi.

Aisha riduwan Muhammad daya ce daga cikin daliban da suka amfana da tallafin karatun ta mika godiyarta ga gidauniyar bisa daukar nauyin karatun su.

wakilinmu salisu mahmud kura ya rawaito mana cewa

Ana saran Kafin kammala karatun, kowanne dalibai a cikinsu zai lakume zunzurutun kudi Naira miliyan biyu da dubu dari biyar (N2,500,000), jimlar kudin bakidaya Naira Miliyan Dari da hamsin (N150,000,000).

Manufar shirin shine samarda karin ma’aikatan jinya da unguwar zoma a Karamar hukumar Bichi da ma Jihar kano domin kara inganta harkar kiyon lafiyar Al’umma.

Start typing and press Enter to search