
An ja han kalin Alumma da suci gaba da baiwa jami’an tsaro Hadinkai domin cigaba da kare rayuka da dukiyoyin su.
kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP Ibrahim Adamu Bakori ne ya bayyana hakan yayin da yakai ziyara ta musamman karamin ofishin ‘yan sanda na Zaura Babba wanda ake kokarin daga darajar ta zuwa baban Ofishin yan sanda da Shugaban Gidauniyar A A Zaura Foundation International Kuma Tsohon dan takarar Sanatan kano ta tsakiya Abdussalam Abdulkarim A A Zaura ya samar domin inganta tsaro a yankin.
CP Ibrahim Adamu Bakori yay aba da Kokarin da A A Zaura keyi wajen yaki da Shaye shaye da harkar daba da kwacen waya ga matasan jihar kano.
Da yake jawabi Amadadin Shugaban gidauniyar A A Zaura Fundation Mataimaki na musaman kan kafafan sadarwar zamani ga Abdussalam Abdulkarim A A Zaura Comr Abbas Hassan Muhammad Bachirawa ya bayyana makasudin kai ziyarar ta kwamishinan a matsayin yunkurin Rundunar yansandan jihar kano na ganin an daga likkafar ofishin yansandan na zaura domin kara samar da tsaro a yankin
Comr Abbas Hassan Muhammad Bachirawa yay i Karin haske kan yunkurin A A Zaura na ganin an dakile harkar shaye shaye da daba a jihar kano.
Akarshe CP Bakori ya godewa Abdussalam Abdulkarim A A Zaura bisa wannan aiki da yadauko tare da bada tabbacin rundunar yansandan jihar kano na ganin an magance duk wata matsala ta tsaro dama harkar daba da shaye shaye a jihar kano.