An zaɓi tsohon Ministan Raya Tattalin Arziki na Mauritania, Sidi Ould Tah, a matsayin sabon shugaban Bankin Raya Ƙasashen Afirka (BADEA). Ya karɓi ragamar shugabancin ne a wani mawuyacin lokaci, inda bankin ke fuskantar barazanar rasa dala biliyan biyar ($5 billion) daga tallafin da Amurka ke baiwa ƙasashen Afirka masu karamin ƙarfi.
A jawabinsa bayan karɓar muƙamin, Sidi Ould Tah ya bayyana aniyarsa ta tabbatar da cewa ƙasashen Afirka sun kasance masu taka rawar gani a harkar kasuwanci da sauran ƙasashen duniya. Ya kuma nuna kyakkyawan fata cewa yawan al’ummar nahiyar Afirka zai zama ginshiƙi wajen bunkasa tattalin arzikinta.
Sidi Ould Tah ya karɓi muƙamin ne daga hannun tsohon shugaban bankin, ɗan Najeriya Akinwumi Adesina.