Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya IPMAN, ta sanar da sabuwar yarjejeniya da matatar man Dangote, wadda za ta rage farashin man fetur zuwa N935 kowace lita. Hakan ya biyo bayan rage farashin man fetur da aka yi a baya-bayan nan a matatar man Dangote, wanda ya baiwa ‘yan kasuwa damar daidaita farashin famfunan su yadda ya kamata. Ana sa ran sabon tsarin farashin zai fara aiki a ranar Litinin mai zuwa, wanda zai kawo sauki ga masu amfani da man da ke kokawa kan tsadar mai a watannin baya-bayan nan.