Farashin kayan abinci a Najeriya ya ƙara tashi daga kashi 33.88 zuwa kashi 34.60, a watan Nuwanba 2024, kamar yadda hukumar kidaddiga ta ƙasar ta sanar a ranar Litinin.
Rahoton hukumar ya ce an samu ƙarin kashi 0.72 cikin dari idan aka kwatanta da na watan Oktoba, 2024.
‘A rahoton shekara-shekara an samu ƙarin kashi 6.40 idan aka kwatanta da na watan Nuwanba 2023,” cewar rahoton.
Ana la’akari da farashin kayan masurufi da suka hada da shinkafa da fulawa da hatsi da busasshen kifi da ƙwai da naman shanu da na rago da kaji da sauransu.
Farashin abinci da na kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabi a Najeriya tun bayan kama mulkin shugaban ƙasar, Bola Tinubu, lamarin da ake ganin shi ne mafi muni da ƙasar ta taɓa faɗawa cikin tun bayan samun ƴanci, kimanin shekara 60 da suka gabata.
Cire tallafin man fetur da barin naira ta tantance darajarta a kasuwa na daga cikin matakan da shugaban ya ɗauka waɗanda ake ganin su ne suka ta’azzara yanayin.
A lokacin da ya karɓi cikin watan Mayun 2023, Tinubu ya ayyana cire tallafin man fetur, lamarin da ya sa farashin fetur ɗin ya zuwa yanzu ya zarta naira 1,000 a wasu sassan ƙasar.
Hakan na nufin ƙarin farashin sufuri wanda shi kuma kan shafi farashin kayan masarufi.