Mummunan hatsarin mota da ya afku a hanyar Kano zuwa Maiduguri, a karkashin gadar sama ta Muhammadu Buhari da ke Hotoro a jihar Kano, ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 23 tare da jikkata wasu 48.

Rahotanni sun baiyana cewa hadarin dai ya rutsa da wata tirela mai dauke da kaya da fasinjoji, bayan da birkin ta ya shanye saboda tsananin gudu, sai kawai ta kife a karkashin gadar.

A cewar kwamandan hukumar kula da tituna, FRSC, reshen jihar Kano Umar Matazu, hatsarin ya afku ne a ranar 13 ga watan Fabrairun 2025 da misalin karfe 9:50 na dare.

Ya ce hukumar FRSC ta aike da jami’ai da ababen hawa zuwa wurin da lamarin ya faru cikin gaggawa domin ceto wadanda lamarin ya shafa.

Kwamandan sashin ya bayyana cewa fasinjojin da abin ya shafa manya 67 ne da yara hudu, jimilla mutane 71.

“Abin takaici, mutane 23 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 48 suka samu munanan raunuka.

“An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Murtala Mohammed domin samun kulawar gaggawa,” in ji shi.