Duk wanda ya fusata ina yi wa Tinubu aiki to ya rungumi taranfoma – Wike

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa yana jin dadin yin aiki da shugaban kasa Bola Tinubu da kuma gwamnatin jam’iyyar All Progressives Congress.

Wike, jigo a jam’iyyar Peoples Democratic Party, kuma dan adawa daya tilo a majalisar ministocin Tinubu, ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a yayin taron jam’iyyar PDP a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.

Tsohon Gwamnan Jihar Ribas ya bayyana cewa har yanzu bai hakura da yin aiki da gwamnatin Tinubu ba, duk da sukar da ake masa bayan nadin nasa.

A cewar ministan, bai yi nadama ba game da matakin da ya dauka, kuma ya gamsu da matsayinsa a gwamnati mai ci.

Ya ce, “Muna cikin gwamnati. Muna cikin cikakkiyar gwamnatin Tinubu. Ba ni da nadama game da shi, kuma zan ci gaba da kasancewa a wurin. Duk wanda ya fusata ya je ya rungume taransfoma.”

Nadin da Wike ya yi a matsayin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja ya haifar da tattaunawa, inda mutane da yawa ke nuna cewa matsayinsa na minista kyauta ce ta gudummawar da ya bayar wajen nasarar da Tinubu ya samu a Jihar Ribas a zaben shugaban kasa na 2023.