
Kimanin Dalibain jami’ar Kimiyya ta babura 24 ne ya asalin karamar hukumar bichi suka amfana da tallafin kudin makaranta.
Wanda (Dr) Abubakar Kabir Abubakar Bichi (FoE) a Jiya Asabar ya amince tare da biyawa wa Daliban kudin makarantar Federal University of Technology Babura dake Jihar jigawa.
Kudin Makarantar har N 4,458, 654.00 domin cigaba da karatunsu na Zangon 2024/2025.
ko a ranar larabar data gabata Saida Danmajalisar na bichi ya dauki nauyin Karatun Daliban aikin jinya da unguwar zoma su 60 a makarantar koyan aikin kiwan lafiya ta plagship dake Bichi
hakan na cikin kudirin Dan majalisar don gain ansamar wa yan asalin Karamar hukumar Bichi wadanda suke Karatu a Dukkanin Makarantun dake gaba da Sakandire Mallakin Gwamnati kudaden karatunsu ba tare da nuna wani bambancin Addini, Yare ko Siyasa ba.
Shugaban Kwamitin Ilimi Dr. Habibu Abdu Bichi ya Kara Yabawa Dr Abubakar Kabir Abubakar Danmajalisar bisa hadin Kai da yake bawa Kwamitin babu dare babu Rana don ganin an tafiyar da harkar Ilimi a Karamar hukumar yadda ya kamata, Kuma ya mika Godiya ta musamman a madadin Sauran ‘yan Kwamitin Ilimin ga Danmajalisar tare da yimasa Addu’ar Allah ya Kara yimasa Jagoranci
A Karshe dai Kwamitin Ilimi yaja hankulan Dukkanin Dalubai dasu zamanto Masu Maida hankali don ganin Kwalliya ta biya kudin sabulu.