Kimanin Daliban Jami’ar Kimiyyya da Fasaha ta Aliko Dangote University of Science and Technology Wudil (ADUSTECH), dubu 18  ne za’a gudanar da taron yaye wa  karo tare da karrama wasu manyan mutane da da Digirin Girmamawa.

Shugaban jami’ar Farfesa Musa Tukur Yakasai ne ya bayyana hakan yayin taron manena labarai da ya gudana a yau talata 6 ga watan mayu 2025, a dakin taro na jami’ar dake Wudil a Kano, yace zasu bawa dalibai sama da dubu 18 masu digiri na farko da masu digiri na biyu na kusan shekara biyar shaidar kammala karatu.

Yakasai ya kuma ce, wannan biki na yaye daliban zai fara daga gobe labara 7 ga watan mayu 2025, zuwa asabar 10 ga wata, yace a yayin bikin Jami’ar za ta karrama wasu manyan mutane tare da bawa Alhaji Aliko Dangote, takardar girmamawa da kuma sandar gudanarwa a matsayin uba ga makarantar a karo ba biyu.

Kazalika yace daga cikin wadanda makarantar zata bawa lambar yabo na digiri, akwai Alhaji Dahiru mangal, da tsohon Gwamnan jihar Kano kuma wanda ya assasa makarantar Eng. Rabi u Musa Kwankwaso, sai Shugaban Rukunin Kamfonin AMASCO Alhaji Mustapha Ado Amasco.

Shugaban jami’ar ya kara da cewa sun shirya tsaf domin gudanar da wannan bukukuwa cikin tsari, sun kuma tanadi dakunan taro wanda gwamnatin Jihar Kano ta gyara wa makarantar, sannan sun tanadi wajan ajjiye manyan baki da dukkan abinda suke bukata yayi taron.

Ya ce, a fannin tsaro sun tanadi Jami ‘an tsaro na makaranta tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro da suka hada da Yan Sanda, Civil Defence, da dai sauran su, domin gudanar da bukukuwan cikin kwanciyar hankali da annashuwa.

A karshe Shugaban Makarantar ya ce suna maraba da daukacin al’ummar jihar kano da na kasa baki daya domin taya daliban da suka kammala karatun murna tare da sanya musu Albarka.