
Hukumar karbar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta kama tare da tsare Daraktan kula da Ma’aikata, da Ma’ajin Kudi na Karamar Hukumar Nasarawa da Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna Mustapha Maifada bisa zargin karkatar da Naira Miliyan 105.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa an umarce su da su baiwa Mustapha Maifada Naira Dubu 105 don gabatar da wani shiri, a maimakon haka sai suka bashi Naira Miliyan 105.
Sai dai sun ce sun baiwa maifada kudin ne bisa kuskure ntun a watan Nuwambar 2024.
An bayyana Mustapha Maifada ya fara kashe kudin da aka tura masa inda aka ce ya sayi kadarori da suka haɗa da gidaje sannan ya canja mota shi da matarsa don holewa.
Hukumar karkashin jagorancin Barr. Muhuyi Magaji Rimin Gado na ci gaba da tsare su don tsaurara bincike.
Don jin karin bayani majiyar Gcmx radio ta tuntubi shugaban hukumar karbar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano Muhuyi Magaji Rimingado, amma bai daga wayar da aka buga masa ba.