Shugaban kanfanin saida maganguna na NOVEMED, Musa Rabiu Kwankwaso, daya kasance ɗan uwa ga sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ƙalubalanci binciken da wasu hukumomin yaƙi da rashawa uku suke gudanarwa a kansa kan zargi ɗaya kuma a lokaci guda.
Musa Kwankwaso wanda yake tare da tawagar lauyoyinsa ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan ya amsa gayyatar da Hukumar Karɓar Korafe-Korafe da Yaƙi da Rashawa ta Jihar Kano tayi masa a Alhamis din nan.
A bayan nan dai ana ta cece-kuce kan wata kwangila wadda ta shafi kai wa ƙananan hukumomin Jihar nan 44 magunguna.
Cece-kucen na zuwa ne bayan ɓullar wani bidiyo da mai barkwanci nan a dandalan sada zumunta, Bello Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello ya fitar, inda yake zargin Gwamnatin Kano da bai wa wani kamfani na Novomed kwangilar siyan magunguna.
A bidiyon, Dan Bello ya yi zargin gwamnatin Kano da bai wa ɗan uwan tsohon Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso kwangilar siyan magungunan inda ya ce a duk wata kowace ƙaramar hukuma ta Kano na bayar da naira miliyan tara ga kamfanin na Novomed mallakar Musa Garba Kwankwaso.
Sai dai kuma Fitar bidiyon ke da wuya, Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya ce ba shi da masaniya kan lamarin, ya bayar da umarni ga hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar kan ta gudanar da bincike nan take sannan ta gabatar da rahoto game da hakan domin ɗaukar mataki.
A cewar hukumar karbar koarafe korafe da yaki da cin hanci da rasahawa ta nan Kano, kawo yanzu an gano naira miliyan 160 daga cikin naira miliyan 440 da ake nema kan kwangilar da ba ta da asali a hukumance.- Optmised for news blog