
Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Kananan Hukumomin Gezawa da Gabasawa Muhammad Chiroma Na Laraba ya taya daukacin Al’ummar musulmi murnar Bikin Sallah Babba.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Shugabar ya fitar kuma ya aikowa Gcmx Radio
Muhammad Chiroma Na Laraba ya tace
“Amadadin al’ummar Kananan Hukumomin Gezawa da Gabasawa Yake taya al’ummar Musulmin duniya musamman jihar Kano da karamar hukumar Gezawa da Gabasawa murnar bikin Babbar Sallah
Ya kara da cewa Suna kara godiya ga Allah da ya nuna mana wannan babbar rana mai daraja, Allah ka maimaita mana ya Allah ka gafarta mana kura-kuren mu, ka karbi kyawawan aiyukan mu.
“Yakara dacewa Ina yiwa Mai girma gwamnan Kano da mataimakinsa Da Jagoran Kwankwasiyya Dr Rabiu Musa Kwankwaso da Sarakunan Kano da Rano da Karaye da Gaya Barka da Sallah da fatan Allah ya maimaita mana ta badi”
A karshe yayi fatan ‘yan uwa musulmai zasu cigaba da yiwa Kasa Najeriya da Jihar Kano addu’a, Allah ya kawo zaman lafiya mai dorewa, tare da fatan samun yalwar arziki da dukiya mai albarka dafatan Allah ya bada damuna mai albarka.