
Shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano Ambasada Haruna Zago ya rasu bayan fama da rashin lafiya.Daya daga cikin ma’aikatan hukumar ne ta tabbatar da Gcmx Radio rasuwar Haruna Zago a asibiti.
A ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2023 gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada Haruna Zago a matsayin Shugaban hukumar kwashe shara ta Kano