Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce ta ware sama da naira biliyan 17 domin inganta lafiya da rayuwar dabbobi a fadin jihar.

Kwamishinan kula da harkokin dabbobi na jihar, Farfesa Abdulrahman Salim, ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kare kasafin kudin da ma’aikatar na shekarar 2026 a gaban kwamitin noma da kiwo na majalisar dokokin jihar a Dutse.

Farfesa Salim ya ce za a yi amfani da kudin wajen gudanar da ayyuka daban-daban da ma’aikatar ta mayar da hankali kan su domin inganta rayuwar dabbobi a shekarar 2026.

Ya ce ma’aikatar ta gabatar da shirin kafa wuraren kiwon dabbobi a fadin jihar, inda za a girke makiyaya da sauran masu kiwon dabbobi.