Shugaba Bola Tinubu ya amince da manufofin kasa kan Hijira na Ma’aikatan Lafiya don magance kalubalen da ke addabar ma’aikatan lafiyar Najeriya.

Ministan lafiya da walwalar jama'a, Farfesa Muhammad Pate, ya bayyana hakan a jawabin sa na X ranar Litinin.

Pate ya ce manufar ba ta wuce mayar da martani ga ci gaba da ficewa daga kwararrun kiwon lafiya ba amma cikakkiyar dabara ce don sarrafawa, amfani, da kuma sauya ƙaura na ma'aikatan kiwon lafiya.

Pate ya ce, “A yammacin yau, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR ya amince da wata muhimmiyar manufa da aka tsara don sauya tsarin kula da albarkatun dan Adam na kiwon lafiya a Najeriya.