Rundunar sojin Najeriya na samun gagarumin sauyi, tare da samun sabbin kayan aiki na yaki kamar motocin yaki masu jure wa nakiya (MRAP), bindigogi, alburusai, da kuma jirage masu saukar ungulu guda biyu kirar BELL UH-1 Huey. Wadannan kayan aikin, wadanda Babban Hafsan Sojojin Kasa (COAS) Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya jagoranta, suna da nufin kara inganta ayyukan sojoji a fadin kasar nan.
Janar Lagbaja, yayin da yake jawabi a taron Kwata na Biyu da na Uku na Shekarar 2024 na Babban Hafsan Sojojin Kasa, ya jaddada irin tasirin da wadannan kayan aiki ke yi a ayyukan sojoji. Ya kuma tabbatar da cewa, jiragen da aka samu, wadanda a halin yanzu ake horas da sojojin Najeriya a kansu, za a fara amfani da su nan ba da dadewa ba wajen gudanar da ayyukan sufuri.
Wannan kokarin sabunta rundunar sojin ya yi dai-dai da hangen nesa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu na gina rundunar soji mai karfi da kwarewa. Janar Lagbaja ya sake nanata kudirin rundunar sojin na ci gaba da zama ba ruwanta da siyasa tare da mutunta ‘yancin dan adam a dukkan ayyukanta.
Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Fasto Umoh Eno, ya yaba da ci gaban da rundunar sojin ta samu tare da jaddada muhimmancin tattara bayanan sirri da kuma hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro. Ya kuma yaba wa COAS bisa jagoranci na gari da ya nuna tare da yin kira ga rundunar sojin da ta ci gaba da bunkasa dabarun da za su tabbatar da nasarorin da ta samu.
A yayin taron, an kuma gabatar da cakokin inshorar rayuwa na rundunar sojin Najeriya ga wadanda suka cancanta, lamarin da ke nuna jajircewar COAS wajen inganta jin dadin sojoji da iyalansu.