Shubagan rukunin kamfanonin Ammasco Alh. Mustapha Ado Muhammad, ya bayyana marigayi Alhaji Ahmadu Haruna Zago a matsayin jajirtacce, mai taimakon na kasa da kuma san cigaban al’umma, wanda ya dade yana bayar da gudummawa a fannoni daban-daban na rayuwa.

Bayanin na kunshe ne a cikin sakon ta’aziya da ya aike ga ‘yan uwa da iyalan marigayin, wanda aka yi jana’izarsa a wannar Juma’ah .

Alh. Mustapha Ammasco, ya kuma mika sakon ta’aziyar wannan rashi ga Gwamnan jihar Engr. Abba Kabir Yusuf da Mai martaba sarkin Kano da kuma al’ummar jihar Kano baki daya.

A cewar sa wannan rashi na Alh. Amadu Haruna Zago, babban rashi ne ga al’ummar jihar kano da kasa baki daya.

“Alh. Amadu Haruna Zago, mutum ne mai san cigaban al’umma, wanda hakan yasa rayuwarsa ta kare akan gwagwarmaya da kwato ‘yancin na kasa”

Haka kuma Alh. Mustapha Ado Muhammad, yace bazai manta da irin gudummawar da marigayin ya ba shi ba a rayuwa ba, a don haka yake addu’ar Allah ya jikansa da rahma yasa aljannace makomar sa, “mu kuma Allah ya kyautata namu karshen” a cewar Alh. Mustapha Ado Muhammad, shugaban rukunin kamfanonin Ammasco.