An ruwaito kashe Salwan Momika mai shekara 38 ne a yammacin ranar Laraba a wani gida a birnin Södertälje.

Zanga-zanga ta ɓarke bayan da Mista Salwan ya ƙona Al-Qur’ani a wajen babban masallacin birnin Stockholm a 2023.

Wata sanarwa da ƴan sandan birnin suka fitar, sun ce an kama mutane biyar, bayan harbe mutumin a daren jiya.

Talla

Kafofin yaɗa labarai sun ruwaito cewa Mista Momika na haska wani abu kai-tsaye a shafukan sada zumunta lokacin da aka harbe shi.

Mista Momika ya kaddamar da zanga-zanga daban-daban na kin jinin Musulunci, abin da ya janyo bore a ƙasashen Musulmi da dama.

Zanga-zanga ta barke a ofishin jakadancin Sweden a Baghdaza har sua biyu, yayin da aka kori jakadan Sweden ɗin daga birnin.

Gwamnatin Sweden dai ta bai wa Momika damar yin zanga-zangar inda ya ƙona Al-Qur’ani, inda ta ce hakan na cikin tsarin dokar ƴancin faɗar albarkacin baki.