Rahotanni daga wasu majiyoyi sun nuna cewa akwai yiwuwar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, zasu haɗu domin kafa wata sabuwar ƙungiya ko haɗin gwiwa a zaben 2027.
Wannan cigaba na iya zama mai girma wajen sauya akalar siyasar Najeriya, musamman idan aka yi la’akari da girman tasirin waɗannan shugabanni a yankunansu da ma ƙasa baki ɗaya. Majiyoyin da ba a bayyana ba sun nuna cewa tattaunawa kan wannan haɗin gwiwa na cigaba, duk da cewa babu tabbacin ko wannan shiri zai kai ga cimma nasara.
Ana tsammanin wannan haɗin gwiwa zai jawo hankalin ‘yan Najeriya da dama, musamman ma magoya bayan PDP da NNPP, inda za su yi nazarin yadda wannan haɗin gwiwa zai iya shafar sakamakon zaɓen 2027. Duk da haka, har yanzu babu cikakken bayanin yadda za a tsara wannan haɗin gwiwa ko kuma irin rawar da kowanne daga cikinsu zai taka idan aka samu cimma yarjejeniya.
Za mu cigaba da kawo muku cikakken bayani da zarar an samu ƙarin haske kan wannan batu.
Abubakar Aminu Daneji
1 Comment
Abubakar Muhammad Sararin Gezawa Rijiyar mangwaro
2 months agoAllah yasa hakan ya haifar mana da Da me ido biyo bayan yadda yan siyasa suke fito sabbin hanyoyin yaudara.