Ina yin Allah wadai da amfani da harsashi mai rai a kan masu zanga-zangar lumana a Kano da Abuja a yau, lamarin da ke tuno da azzaluman gwamnatocin sojoji. Yana da matukar muhimmanci ga gwamnati da hukumomin tsaro su kiyaye aikinsu na tabbatar da kyakkyawan yanayi na zanga-zangar lumana.
Rikicin da ake yi wa masu zanga-zangar da ba su ji ba ba su gani ba, na kara rura wutar tashin hankali ne da kuma kawo cikas ga zanga-zangar lumana. Ina kira ga hukumomin kasa da kasa irin su Majalisar Dinkin Duniya da ICC da su sanya ido sosai a kan al’amuran da ke faruwa a Najeriya tare da dora wa shugabanninta hukunci.
Ina ƙarfafa masu zanga-zangar su ci gaba da yin amfani da yancinsu cikin lumana tare da yin watsi da duk wani nau’i na tashin hankali. Wadanda suke da hannu wajen wawure dukiyar jama’a da barnata dukiyoyi su fuskanci hukuncin shari’a, domin wadannan ayyuka na dakushe sahihancin zanga-zangar.
Dole ne shugaba Tinubu ya nuna jagoranci ta hanyar magance bukatun al’ummar Najeriya cikin gaggawa.
Atiku Abubakar X