A ranar Juma’a, na gabatar da wata takarda ga Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa inda na sanar da ofishina cewa zan tafi hutun rashin iyaka domin magance matsalolin lafiya da ke addabar iyalina.
Duk da cewa na fahimci cewa jirgin kasa ba ya jiran kowa, wannan mataki mai raɗaɗi – wanda ya haɗa da dakatar da ayyukana a matsayin Mai Ba da Shawara na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Kafafen Yaɗa Labarai da Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa; Jakadan Musamman na Shugaban Kasa kan Sauyin Yanayi, da Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Shugaban Kasa kan Project Evergreen – an ɗauka ne bayan tattaunawa mai zurfi da iyalina tsawon kwanaki da suka gabata yayin da wani yanayi na rashin lafiya ya tsananta a gida.
Ina fatan komawa aiki na ƙasa cikakken lokaci idan lokaci, waraka, da ƙaddara suka ba da dama.
Ina roƙon a ba iyalina da ni ɗan sirri a wannan lokaci.
Chief Ajuri Ngelale