Tinubu ya kori ministoci biya
A ranar Laraba ne shugaba Bola Tinubu ya kori ministoci biyar daga cikin ministocinsa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan kafafen sadarwa na zamani, Dada Olusegun, ya fitar ranar Laraba.
Ministocin da abin ya shafa sun hada da ministar harkokin mata, Uju-Ken Ohanenye; Ministar yawon bude ido, Lola Ade-John; Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman; Karamin ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Muhammad Gwarzo; da kuma ministar ci gaban matasa, Dr. Jamila Bio Ibrahim.
Sanarwar ta kuma sanar da sake nada wasu ministoci 10 kan sabbin ministocin; nadin sabbin ministoci bakwai don mikawa majalisar dattawa don tantancewa; nadin Shehu Dikko a matsayin shugaban hukumar wasanni ta kasa; nadin Sunday Akin Dare a matsayin mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin sadarwa da wayar da kan jama’a da ke aiki daga ma’aikatar yada labarai da wayar da kan jama’a ta kasa.
An nada Bianca Odumegwu-Ojukwu a matsayin karamar ministar harkokin waje, yayin da Jumoke Oduwole aka nada ministar masana’antu, kasuwanci da zuba jari.
An nada Dokta Nentawe Yilwatda a matsayin Ministan Agaji da Rage Talauci yayin da Muhammadu Maigari Dingyadi ya zama Ministan Kwadago da Aiki.
An nada Idi Mukhtar Maiha a matsayin Ministan Dabbobi. An nada Yusuf Abdullahi Ata a matsayin karamin minista a ma’aikatar gidaje da raya birane, sai kuma Suwaiba Said Ahmad a matsayin karamar ministar ilimi.