Shugaban kungiyar Hizbullah Hassan Nasrallah ya sha alwashin ci gaba da kai hare-hare kan matsugunan arewacin Isra’ila, ba tare da la’akari da daukar fansa ba. Wannan sanarwar ta zo ne bayan hare-haren da Isra’ila ta kai a baya-bayan nan kan ababen more rayuwa na Hizbullah. Sayyid Nasrallah ya yi ikirarin cewa wadannan hare-haren ba za su sa kungiyarsa ta aiwatar da ayyuka a nan gaba ba
Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Lebanon ya bayyana cewa Isra’ila ta kai hare-hare akalla 52 a kudancin kasar ranar Alhamis da daddare, kuma ita ma Lebanon ta mayar da martani da inda ta kai hare-hare kan cibiyoyin soji a arewacin Isra’ila.
Tun da farko shugaban na Hezbollah Hassan Nasrallah, ya ce da hare-haren da Isra’ila ta kai ta na’urorin sadarwa da wayoyin oba-oba da suka rika fashewa, ta keta dukkanin wanta iyaka, a tsakaninsu, yana ma zargin Isra’ilar da kaddamar da yaki.
A jawabin da ya gabatar da aka watsa ta talabijin a jiya Alhamis, shugaban ya ce abin da Isra’ila ta yi ta nuna ba ta damu da komai ba, na dacewa ko rashin dacewa ko mutunta doka ko take ta, ko ma sanin ya kamata.
Ya kara da cewa abin da ta yi kisan kiyashi ne, da kutse a kan Lebanon da al’ummarta, da ‘yancinta da tsaronta, za kuma a iya kiran hakan miyagun laifukan yaki – ya ce duk abin da mutum ya zabi ya kira shi ya dace – domin niyyar abokan gabatar ke nan.
Jagoran na Hezbollah duk da cewa ya yarda hare-haren fashewar na’urorin da suke zargin Isra’ila da kai wa a Lebanon, illa ce a gare su, amma ya kafe cewa tasirinsu takaitacce ne.
Da yake magana da BBC, a kan lamarin tsohon jakadan Isra’ila a Amurka, Michael Oren, ya ce Isra’ila na wani yanayi ne na tsaka-mai-wuya;
“Idan ba maslaha ta diflomasiyya, Isra’ila ba ta da wani zabi , ba ta da wani zabi da ya wuce ta kora Hezbollah baya daga kan iyaka, saboda idan dai har Hezbollah, tana nan a wajen wannan iyaka, ‘yan Isra’ila 100,000 ba za su iya komawa gida ba, ba kuma za su yarda su koma gida ba idan Hezbollah, tana daya bangaren katangar.”
Hassan Nasrallah dai ya lashi takobin cewa Isra’ila za ta dandana kudarta a kan harin, to amma kuma ya kara nuna cewa Hezbollah ba wai tana son rikicin da Isra’ila ya ci gaba ba ne.
Ya ce hare-haren da kungiyarsa ke kai wa cikin Isra’ila za su ci gaba har sai an dakatar da bude wuta a Gaza, kuma ya ce ba wani kisa da za a yi musu da zai sa jama’ar Isra’ila komawa arewacin kasar.
Isra’ila dai ba ta fito fili ta dauki alhakin hare-haren ba na ranar Talata da kuma Laraba, inda na’urorin suka rika fashewa a lokaci guda a fadin kasar ta Lebanon, inda hukumomin Lebanon din suka ce harin ya hallaka mutum akalla 37 tare da raunata wasu 3,000.
Duk da cewa Israi’lar ba ta fito fili ta dauki nauyin kai harin ba, amma ministanta na tsaro Yoav Gallant ya ce kasarsa ta bude wani sabon babi na yaki, inda za ta mayar da hankali kan kare arewacinta.
Yakin kan iyakar da Isra’ilar ke yi da Hezbollah, ya tsananta ne ranar 8 ga watan Oktoba, 2023 kwana daya bayan da Hamas ta kai wa Isra’ila harin bazata – inda Hezbollah ta harba makaman roka kan Isra’ila domin nuna goyon bayanta ga Falasdinawa.
Tun daga sannan an kashe daruruwan mutane yawanci mayakan Hezbollah a yakin kan iyakar, sannan dubbai sun bar muhallinsu a dukkanin bangarorin biyu – wato na Lebanon da kuma arewacin Isra’ila.
Hezbollah ta ce tana goyon bayan Hamas ne – inda dukkanin su biyun da Iran ke mara wa baya – Isra’ila da Birtaniya da sauran wasu kasashe musamman na yammacin duniya suka ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya yi kira ga dukkanin bangarorin rikicin da su mayar da wuka kube. Yana mai cewa ba sa son ganin rikicin ya ta’azzara da zai sa a kasa cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta a Gaza.