Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Pakistan ta kama wani dan Najeriya a filin jirgin saman Lahore da laifin safarar hodar iblis.
A cewar kafar yada labarai ta Pakistan, Express Tribune a ranar Alhamis, wanda ake zargin wanda ya taho daga Najeriya ta kasar Dubai, an ce ya hadiye capsules 38 dauke da hodar iblis.
A cewar mai magana da yawun ANF, capsules sun ƙunshi jimillar gram 608 na hodar iblis.
A shekarar 2023, hukumomin Pakistan sun kama wasu ‘yan Najeriya 10 a irin wannan hali, inda suka kwace jimillar kwayoyi masu nauyin kilogiram 4.811.
A bana, ANF ta gudanar da ayyuka bakwai, inda aka kama wasu ‘yan Najeriya 8 tare da kwato kilogiram 11.420 na kayan maye.
Wanda ake zargin zai fuskanci tuhuma a karkashin dokar hana shan miyagun kwayoyi, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.