Kinshasa, Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo – Rahotanni sun ce ƙasashen Afirka sun ƙara ƙaimi a kan iyakokinsu da zimmar daƙile yaɗuwar annobar cutar ƙyandar biri, wadda ta yi barazana ga lafiyar mutane a fadin nahiyar.
Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, wadda ta fi fama da cutar, ta sanar da shirin rigakafin cutar da take fata zai daƙile ta. An gano sabon nau’in ƙwayar cutar, Clade1 MPXV, a watan Satumban 2023 a ƙasar. Ministan Lafiya Roger Kamba ya ce gwamnati na ƙoƙarin kashewa da kuma daƙile yaɗuwar cutar, kuma za a ƙaddamar da tsarin rigakafin nan gaba kaɗan.
“Mataki na gaba shi ne, a cewar ministan lafiya, kare yaɗuwar cutar: fito da tsarin yin rigakafin ƙyandar biri a Kongo wanda aka samar kuma aka amince da shi. Yanzu haka ana aikin inganta bin sawun da kuma tsaron daƙile ta a kan iyakoki,” in ji rahoton.
Hukumar daƙile yaɗuwar cutuka ta Afirka, Africa Centre for Disease Control (CDC), ta ayyana ƙyandar birin a matsayin larurar da ke buƙatar kulawar gaggawa a nahiyar ranar 13 ga watan Agusta bayan ta karaɗe ƙasashe 16, ciki har da waɗanda ba su taɓa ganin cutar ba kamar Burundi, da Rwanda, da Uganda, da kuma Kenya.
Kwana ɗaya bayan haka, ita ma Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana ta larurar gaggawa a ƙasashen duniya. Tuni aka gano nau’in cutar a ƙasar Sweden.
Najeriya ta ƙara ƙaimi a kan iyakokinta wajen tantance masu shiga bayan mutum 39 sun kamu a jihohin ƙasar 33 cikin 36. Zuwa yanzu ba a samu rahoton mutuwa ba a ƙasar tun bayan ɓarkewar cutar a wannan karon.
Hukumomin lafiya sun ce za su ƙaddamar da matakai irin waɗanda aka ɗauka a loakcin annobar korona domin daƙile yaɗuwarta a Najeriya. Gwamnati ta ce za a buƙaci duka matafiyan da ke fita daga ƙasar su cike wani fom ta intanet.
Ma’aikatar lafiya ta shawarci jama’a su dinga kula da tsafta, kamar wanke hannu da sabulu, ko kuma amfani da man goge hannu na sanitiser.