Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa, EFCC, Ola Olukayode, ya ce Naira biliyan 50, (N50bn), da aka bai wa asusun lamuni na ilimi na Najeriya, NELFUND ba gudumuwa ba ne daga hukumar, amma wani bangare ne na kudaden da aka kwato na aikata laifuka.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta samu daga shafin ta na Facebook.