Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa gwamnatinsa zata cigaba da ayyuka da mahimman abubuwa wadda Tsohon Shugaban Kasa marigayi Muhammadu Buhari, ya tsaya, yayinda yace zai cigaba a daga inda ya tsaya.
Shugaban ya faɗi hakan ne a ranar Litinin a Abuja, yayin ƙaddamar da littafin tarihin Buhari da Dr Charles Omole ya rubuta.
Hallau yace mafi girman girmamawa da za’a yiwa marigayi shugaba Buhari ita ce ci gaba da ayyuakan shugabancinsa daga inda ya tsaya.
Tinubu Ya bayyana cewa littafin na nuni akan tarihin Buhari cikin adalci, yayin bayani kan nasarori da kuma kura-kurai, tare da ƙarfafa shugabanni da suyi koyi kan darussa daga rayuwar marigayin.
Shugaban ƙasar ya kuma waiwayi doguwar tafiyarsa ta siyasa tare da Buhari, inda ya bayyana shi “A matsayin ɗan’uwa, aboki, kana Kuma abokin tafiya a siyasa.”
Hakazalika Ya ce “Mun gina babbar haɗaka ta siyasa wadda ta kai ga nasarar zaben 2015, inda aka kayar da shugaban ƙasa mai ci a lokacin, lamarin da ya sauya yanayin siyasar Najeriya.”
Tinubu ya jaddada cewa haɗin kai a siyasa ba rauni ba ne, face hikima wajen gina ƙasa.
Hallau ayayin taron, gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yabawa Shugaba Tinubu kan tsayawa tare da iyalan Buhari da kuma jihar Katsina, yana mai bayyana Buhari a matsayin mutum mai ladabi da kishin ƙasa da shugabanci nagari.
Marubucin littafin, Dr Charles Omole, ya ce littafin ya tattaro tarihin rayuwar Buhari tun daga haihuwa har zuwa rasuwarsa, tare da shaidu daga mutanen da suka yi aiki tare da shi.


