Yan Najeriya sun wayi gari ranar Talata da sabon ƙarin kuɗin kiran waya da na data daga kamfanonin sadarwa, inda ƙarin ya rubanya sau uku kwatankwacin kaso 150. Wani abin da ke baƙantawa yan Najeriya rai shi ne yadda suka wayi gari da ƙarin ba tare da sanarwar yin hakan ba kamar yadda suka saba a baya ba, duk da daga baya kamfanin MTN ya nemi afuwa. Masu sharhi kan al’amura na cewa ƙarin kuɗin zai ƙara jefa yan Najeriya cikin halin matsi bisa lura da yanayin da yan ƙasar ke ciki tun bayan ɓullo da jerin matakan tattalin arziki da gwamnatin ƙasar ke yi da suka haɗa da haraje-haraje.
Nawa ne ƙarin da aka yi?
Duk da cewa da ma yan Najeriya na zaman jiran kamfanonin sun yi ƙarin kuɗin kiran da na data kamar yadda hukumar kula da sadarwa ta Najeriya, NCC ta amince wa kamfanonin su yi amma kada ya wuce kaso 50 cikin 100 na farashin. BBC ta fahimci cewa kamfanin MTN ya sauya farashin data misali tsarin 15GB a mako guda daga naira 2,000 zuwa naira 6,000. Dangane da kuɗin kiran waya, BBC ta fahimci cewa MTN na ɗaukar kwabo 75 a kan kowace daƙiƙa maimakon kwabo 13 da kamfanin ke yi a baya. A shafinsa na X, MTN ya ce “sun yi ƙarin ne domin kyautata aiki” sannan kamfanin ya nemi afuwar yan ƙasar cewa “muna neman gafararku dangane da irin tasirin da al’amarin zai yi a kanku da kuma jan ƙafa wajen sanar da ku halin da ake ciki.” Masu amfani da layin Airtel suna ta faman kunfar baki a kafafen sada zumunta inda suka ce kamfanin ya ruɓanya farashin sau fiye da biyu. Sai dai har kawo yanzu ba a ji kamfanin ya ce uffan ba. Sai dai kuma ba a ji masu amfani da kamfanin Glo ba na nuna takaicinsu ba, wani abu da ke nuna cewa wataƙila sai nan gaba kamfanin zai yi ƙarin.
Wane tasiri ƙarin zai yi?
Mubarak Uniquepikin wanda mai yin shirye-shirye ne a shafukan intanet ya shaida wa BBC cewa ƙarin kuɗin kiran waya da na data ka iya yin babban tasiri musamman ga mutanen da ke gudanar da harkokin kasuwancinsu a intanet. “Tattalin arziƙin da ma yana tangal-tangal kuma zuwan wannan ƙarin a yanzu lokacin da jama’a ke kasuwancinsu a shafukan intanet saboda mutane da dama ba sa iya karbar hayar shaguna, zai yi muni ƙwarai.” “Matasa da dama ba sa iya sayen data kuma yanzu wannan ƙarin zai ƙara ta’azzara al’amarin gare su.” In ji Mubarak.
Me ƴan Najeriya ke cewa?
Yanzu haka dai babu wani batu da ake tattaunawa a kai a Najeriya kamar na ƙarin kuɗin wayar da data da kamfanonin suka yi. Mun duba wasu shafukan sada zumunta domin ganin abin da jama’a ke faɗi kamar haka: