Wasu ƴanbindiga sun yi awon gaba da matafiya 28 daga garin Zak da ke yankin Bashar a ƙaramar hukumar Wase da ke jihar Filato.

Wani mazaunin karamar hukumar wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, inda ya ce mutanen da aka sace, da suka haɗa da maza da mata da yara na hanyar su ta zuwa garin Sabon Layi ne domin halartar taron Maulidi a karshen mako.

Ya kara da cewa bayan wayewar garin ne kuma mutane da ke bin hanyar suka ga mota a kan titi, motar wani shugaban al’ummar Zak. Bayan bincike ne aka gane ita ce motar da ke ɗauke da matafiyan

Wani mazaunin garin ya kuma shaida wa gidan jaridar cewa zuwa yanzu babu labarin inda mutanen suke.
Mai magana da yawun ƴansandan ƙasar SP Alabo Alfred ya ce suna bincike kan rahoton faruwar lamarin.