Ukraine ta ci gaba da kai hare-hare zuwa yankin Kursk na kan iyakarta da Rasha a rana ta biyu.
Gwamnan yankin Kursk a Rasha, Alexey Smirnov, ya ayyana dokar ta-ɓaci sakamakon kutsen da Rasha ke zargin sojojin Ukraine da yi mata.
Mista Smirnov ya kira lamarin ‘mai sarƙaƙiya’
Tun da farko shugaban Rasha, Vladimir Putin ya zargi Ukraine da abin da ya kira ”ƙarin takalar faɗa”, bayan da jami’an tsaron Rasha suka ce sojojin Ukraine sun kutsa yankin Kursk a ranar Talata.
Rasha ta ce sojojin na Ukraine cikin tankokin yaƙi 11 da motocin sulke fiye da 20 sun tsallaka kan iyaka zuwa kusa da garin Sudzha, mai nisan kilomita 10 daga filin daga.
Cikin wani jawabi da ya yi ta gidan talbijin, Babban hafsan tsaron Rasha, Janar Valery Gerasimov ya shaida wa Shugaba Putin cewa sojojin Rasha sun dakatar da ”dannawar dakarun na Ukraine zuwa yankin, bayan da suka kai hari don lalata wasu ababen hawa da makaman nasu a kusa da kan iyakokin ƙasashen biyu.
Wannan hari ka iya zama ɗaya daga cikin hari mafi ban mamaki da Ukraine da kai yankunan Rasha, tun bayan mamayar da Moscow ta yi wa ƙasar cikin watan Fabrairun 2022.
Labaran BBC