Tsohon Gwamnan jihar Jigawa alhaji Sule Lamido yace matsawar jam’iyyarsu ta PDP taki warware rikice rikicenta zai kulla kawance da wata jam’iyyar
Alhaji Sule Lamido, kuma nuna matuƙar takaicinsa kan yadda wasu ke ƙoƙarin ganin an rusa jam’iyyar PDP gaba ɗaya.
Cikin wata hira da ya yi da BBC, tsohon gwamnan Jihar Jigawa ya ce idan abubuwa suka ci gaba da tafiya ba daidai ba, zai ɗauki matakin da ya ga ya fi dacewa da shi.
Jam’iyyar PDP dai na fama da rikicin cikin gida, lamarin da ya sa ta rasa wasu gwamnoni, ’yan majalisu da kuma manyan jiga-jiganta, sakamakon rikicin da ya daɗe yana ci ba tare da samun maslaha ba.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen fara kaɗa harkokin siyasa gabanin zaɓukan shekarar 2027.


