Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ce kamata ƴan Najeriya su mayar da hankali wajen zaɓen shugaban ƙasa da ya cancanta a zaɓe mai zuwa, a madadin karkata ga yankin da shugaban zai fito.
Malam Shekarau ya ce batun yankin da shugaban ƙasa ya fito ba shi da wani muhimmanci a tsarin shugabanci na gari.
Da ya ke tsokaci game da kiraye-kirayen mayar da mulkin Najeriya ga wani ɓangare na ƙasar a hirar sa da gidan talabijin na Channels a Najeriya, Malam Shekarau ya ce “Ya kamata jam’iyyu su fitar da tsari mai kyau na zaɓen wanda ya fi cancanta a tsakanin ƴan takara. Wannan zai bai wa ƴan Najeriya damar darjewa a tsakanin su, domin zaɓen wanda ya fi dacewa da zama shugaban ƙasa”
An shafe watanni ana muhawara a kan kiraye-kirayen mayar da mulki arewacin Najeriya a shekarar 2017.
Sai dai masu adawa da hakan sun ce yankun kudanci da shugaba Bola Tinubu ya fito bai kammala wa’adin sa na shekara takwas ba, don haka Arewa ta jira sai ya kammala.
Amma tsohon gwamnan jihar Kano na ganin cewa ya kamata a mayar da hankali wajen zaɓen shuagabanni na gari da za su yi wa ƙasa aiki.
Source : BBC