Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da ƙarin sabbin haraji ga ƙasashen duniya a ranar Laraba, yana mai cewa matakin zai taimaka wa Amurka ta bunƙasa tattalin arziƙinta. Sai dai, masana sun yi hasashen cewa wannan mataki na iya jefa tattalin arziƙin duniya cikin matsala.
Trump ya bayyana cewa, ya zama dole a ɗauki wannan mataki domin daidaita harkokin kasuwanci tsakanin Amurka da sauran ƙasashen duniya, da kuma kare ayyukan yi da masana’antu na Amurka.
Ƙasashen Afirka Da Harajin Ya Shafa:
- Lesotho – 50%
- Madagascar – 47%
- Mauritius – 40%
- Botswana – 37%
- Afirka ta Kudu – 30%
- Najeriya – 14%
- Kenya – 10%
- Ghana – 10%
- Ethiopia – 10%
- Tanzania – 10%
- Uganda – 10%
- Senegal – 10%
- Liberia – 10%
Ƙasashen Da Aka Ɗora Wa Harajin 10%:
Amurka za ta sanya haraji na 10% ga dukkan kayayyakin da ake shigo da su Amurka, wanda ake sa ran zai fara aiki a ranar 5 ga watan Afrilu. Ƙasashen da za su fuskanci wannan harajin sun haɗa da:
- Burtaniya
- Singapore
- Brazil
- Australia
- New Zealand
- Turkiyya
- Colombia
- Argentina
- El Salvador
- Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa
- Saudiyya
Harajin Ramuwar Gayya:
Amurka ta kuma lafta harajin ramuwar gayya kan wasu ƙasashe, wanda zai fara aiki a ranar 9 ga watan Afrilu. Waɗannan ƙasashe sun haɗa da:
- Tarayyar Turai: 20%
- China: 54%
- Vietnam: 46%
- Thailand: 36%
- Japan: 24%
- Cambodia: 49%
- Afirka ta Kudu: 30%
- Taiwan: 32%
Canada Da Mexico Ba Su Cikin Waɗanda Abin Ya Shafa:
Harajin na 10% bai shafi ƙasashen Canada da Mexico ba, duk da cewa da farko su ne waɗanda Trump ke haƙo.
Harajin Motoci:
Trump ya kuma tabbatar da cewa harajin 25% a kan dukkan motocin da ake shigo da su Amurka ya buɗe sabon babi na sabuwar Amurka, kuma zai fara aiki nan take.