Ranar Arfa ba kawai rana ce da ake tsayuwa a Arafat ba – ita ce rana da Allah ke alfahari da bayinSa a gaban mala’iku. Manzon Allah (SAW) ya ce:

“Babu wata rana da Allah ke yawan ‘yantar da bayinSa daga wuta kamar ranar Arfa.” (Sahih Muslim)

Azumin wannan rana ga wanda ba ya aikin Hajji yana da falala mai tarin yawa:

  • Kaffarar zunuban shekara guda da ta gabata, da kuma shekara guda mai zuwa.
  • Nuni da biyayya da ƙauna ga Allah.

SHIN WANE NE YA KAMATA YA AZUMTA?
Dukkan Musulmi da suka balaga kuma ba su da wata matsala ta lafiya suna iya yin wannan azumi. Amma ga masu aikin Hajji, Manzon Allah (SAW) bai azumci ranar Arfa ba domin ya kasance a cikin tafiya da ibadar Hajji.