Masana’antar Man Fetur ta Dangote ta rage farashin man fetur daga N950 zuwa N890, da ragewar da za ta fara aiki daga Asabar, 1 ga Fabrairu, 2025.
Matatar man Dangote ta rage farashin man fetur daga naira 950 zuwa 890, inda ragin ya fara aiki tun daga jiya Asabar 1 ga watan Fabarairun 2025.
A bayanin da matatar ta fitar ta nuna cewa ta yi ragin ne saboda raguwar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.
Matatar ta ce hakan na daga ƙudurinta na tabbatar da gaskiya da adalci a harkar, a duk lokacin da aka samu rangwame a kasuwar duniya ita ma ta yi hakan ta yadda al’umma za su amfana.
Ta kara da cewa ta yi amanna ragin zai sa a samu saukin farashin a faɗin Najeriya, wanda hakan ta ce zai sa a samu saukin farashin kaya da ayyuka da saukin rayuwa gaba ɗaya.
Matatar ta kuma yi kira ga ‘yankasuwa masu sayar da man da su bayar da hadin kai ta wannan fanni domin ganin al’ummar Najeriya sun amfana da sauƙin.