Hukumar Harajin Ƙasa (FIRS) ta sanar da cewa Lambar Shaidar Ƙasa (NIN) da Hukumar NIMC ke bayarwa ita ce za ta zama Lambar Haraji (TIN) ga dukkan ‘yan Najeriya. Wannan sanarwa ta fito ne a ranar Litinin ta shafin X, a wani shirin wayar da kai kan sabon tsarin haraji.
Hukumar ta kuma bayyana cewa kamfanoni ba za su sake buƙatar TIN na musamman ba, domin Lambar Rajistar Kamfani (CAC) ita ce za ta zama shaidar haraji a sabon tsarin.
FIRS ta ce dokar Nigeria Tax Administration Act (NTAA) da za ta fara aiki a Janairu 2026, ta tanadi amfani da Tax ID a muhimman mu’amaloli kamar buɗe asusun banki. Ta ƙara da cewa wannan tsari ba sabon abu ba ne, tun da ya fara aiki tun Finance Act na 2019, sai dai yanzu an ƙarfafa shi.
Hukumar ta ce tsarin zai taimaka wajen sauƙaƙe tantance masu biyan haraji, hana karkatar da haraji, da tabbatar da adalci, tare da roƙon jama’a su yi watsi da jita-jita ko labaran ƙarya game da sabon tsarin.


