Gwamnan jihar Kano ta kaddamar da wata kasuwar shanu ta kasa da kasa a Dambatta ta miliyoyin kudi da aka inganta ta hanyar hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da bankin cigaban Musulunci na jihar Kano da ke tallafawa ayyukan noma da makiyaya.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Tofa, ya fitar a ranar Asabar.
Sanarwar ta ce, “Kasuwar Shanu ta Dambatta na daya daga cikin kasuwanni biyar da aka inganta, wadanda suka hada da Tsanyawa, Falgore, Doguwa da Wudil, bi da bi.
“A kowace kasuwannin guda biyar, Gwamnatin jihar ta samar da hanyoyin lodi, kayayyakin ruwa, dakunan kwana na ofis na bayanan kasuwa, wuraren tsaro, kayayyakin aikin kiwon dabbobi, abubuwan jin dadin jama’a, da kuma wutar lantarki domin tsaro don yin kasuwanci ko da a cikin duhu ne.”