Jam’iyyar PDP reshen jihar Jigawa ta nuna rashin jin daɗi kan matakin dakatar da Sule Lamido, CON, daga ayyukan kwamitin amintattu na jam’iyyar,tana mai kira da a gaggauta janye hukuncin.

A wata sanarwa da shugaban PDP na Jigawa, Babandi Ibrahim Gumel, ya fitar, jam’iyyar ta bayyana dakatarwar a matsayin rashin adalci,kuma hakan zai ƙara rarraba kan jam’iyya, musamman a lokacin da ake buƙatar haɗin kai domin fuskantar jam’iyyar APC mai mulki.

Ya ce zargin da aka jingina wa tsohon gwamnan na halartar wasu tarurruka da ake ganin barazana ne ga haɗin kan jam’iyyar ba hujja ba ce, domin Lamido ya yi abin da doka da kundin tsarin mulki suka ba shi dama.