Jami’an ’Yan Sanda biyu sun rasa rayukansu yayin da wata arangama da ta ɓarke tsakaninsu da mabiya ɗariƙar Shi’a (IMN), a kasuwar Wuse da ke Abuja.
Kazalika, an harbe wani ɗan kasuwa mai suna Amiru, yayin da yake ƙoƙarin tserewa lokacin ta tarzomar ta tashi, inda daga bisani ya rasu a hanyar zuwa asibiti.
Rikicin dai ya fara ne lokacin da ’yan Shi’a da ke gudanar da tattaki suka yi arangama da ’yan sanda.
Sun yi wa jami’an ƙawanya, inda suka ƙwace makamansu, sannan suka ƙone motocin ’yan sanda uku.
A martanin da rundunar ’yan sandan Abuja, ta mayar kan lamarin, ta bayyana harin a matsayin abun takaici.
Amma rundunar ta tabbatar da cewa an kama mutane da dama da ke da alaƙa da rikicin.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yansandan babban birnin SP Josephine Adeh, ta fitar, ta tabbatar da kisan jami’ansu guda biyu da jikkata wasu biyu tare kuma da kona motocin ‘yansanda na sintiri uku a rikicin wanda ta ce ba gaira ba dalili mabiya kungiyar suka kai wa jami’ansu hari.
Kwamishinan ’yan sandan Babban Birnin Tarayya, CP Benneth C. Igweh, ya yi Allah-wadai da tashin hankalin.
Ya kuma lashi takobin gurfanar da waɗanda suka aikata laifin a gaban kuliya.