ta ƙone shaguna da kayayyaki masu yawa, lamarin da ya janyo asara mai tsanani ga ‘yan kasuwa da dama.Gobarar ta faru ne a daren Litinin, bayan ‘yan kasuwa sun rufe kasuwancinsu, kuma ta durƙusar da sana’o’in mutanen dake dogaro da kasuwar wajen samun abin rayuwa.Gwamnan jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana alhini da jimami matuƙa bisa faruwar lamarin.A cikin wata sanarwa da Darakta-Janar na harkokin yaɗa labarai na gwamnatin jihar, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi da juyayi ga al’ummar da abin ya shafa, tare da miƙa saƙon jaje ga dukkan ‘yan kasuwa da masu shagunan da gobarar ta rutsa dasu.Sanarwar ta ce “Gwamna Inuwa ya tabbatar wa waɗanda abin ya shafa cewa gwamnatin jihar na tare dasu a wannan lokaci mai wahala, inda ya umarci hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar (SEMA) da sauran hukumomi masu alaƙa dasu da su hanzarta bincike kan musabbabin gobarar, tare da kai tallafi da agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa.Gwamnan ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatinsa na kafa wata cibiyar kwana-kwana ta zamani mai kayan aiki na ƙwarewa domin ƙarfafa kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.


