An hana Daliban Najeriya 161 shiga Burtaniya.
A kalla dalibai 1,425 na kasa da kasa da suka sami shiga jami'o'i a Burtaniya an hana su shiga a filayen jirgin saman kasar tsakanin 2021 da 2023.
‘Yan Najeriya 161 ne abin ya shafa, yayin da aka kwashe su a tashoshin jiragen sama na kasar Burtaniya.
Alkaluman da aka samu musamman daga ofishin kula da harkokin cikin gida na Burtaniya ta hanyar dokar ‘yancin bayanai, Indiya ce ta kan gaba a jerin daliban kasashen waje da abin ya shafa da 644, wanda ke wakiltar kashi 45 cikin 100 na adadin, yayin da Najeriya ke biye da kashi 11.3 cikin 100. Ghana ce ta uku a jerin kasashe da kashi 92 (6.46%), yayin da Bangladesh ke matsayi na hudu da kashi 90 (6.32%).
Koyaya, bayanan da aka fitar, wanda ya shafi Oktoba 2021 zuwa Oktoba 2023, sun iyakance ga ɗaliban da aka hana su shiga a filayen jirgin sama. Ba ya haɗa da ɗaliban ƙasashen waje da Ofishin Cikin Gida ya kora saboda karya sharuddan bizar su, kamar aiki fiye da sa'o'i 20 a mako-mako da kuma rashin aikin koyarwa.