Yaƙin kasuwancin duniya da ake yi kan haraji ya sake haifar da halin ha’ula’i a kasuwannin hannayen jari na duniya. Kasuwannin Turai da na Asiya sun shiga cikin yanayi mai hatsari, inda masu sharhi suka bayyana cewa masu zuba jari na bukatar ƙarin kuɗaɗe, ko kuma sun fara ganin zuba jari a kamfanonin Amurka na da haɗari.

Wannan halin ya faru ne saboda ƙaruwar cece-kuce tsakanin manyan tattalin arziƙin duniya, musamman Amurka da China, kan batutuwan haraji da kasuwanci. Ana ganin China, ɗaya daga cikin manyan masu bin Amurka bashi, na daga cikin waɗanda ke kan gaba wajen sayar da takardun lamuni na Amurka, wanda ke ƙara ƙarin damuwa a kasuwannin.

Masana tattalin arziƙi sun yi gargadin cewa ƙaruwar bashin da ake bin gwamnatin Amurka na iya yin illa ga bangaren ba da bashin gidaje da kuma ƙara yawan kuɗin ruwa, wanda zai iya shafar tattalin arziƙin duniya gaba ɗaya.

Wannan halin ha’ula’i ya sanya masu zuba jari cikin damuwa, yayin da suke ci gaba da bin diddigin yanayin da ke faruwa a kasuwannin duniya.

https://www.bbc.com/hausa/live/c4g99l4ggl5t?post=asset%3Ae5fb8b89-7589-445b-bed2-54026b836678#asset:e5fb8b89-7589-445b-bed2-54026b836678