George, wanda ya shiga makarantar horar da matasa ta Chelsea tun yana dan shekara takwas, ya nuna kwazo a wasan da suka yi a Poland. Ya zura kwallonsa ta farko a babban wasa bayan da aka tura bugun daga kai mai nisa da Reece James.
“Ina matukar farin ciki da zura kwallo, na yi matukar jin dadi,” in ji George, dan wasan Ingila ‘yan kasa da shekaru 19. “Na buga wasanni da yawa a yanzu amma yana da kyau in samu kwallona ta farko.”
Maresca ya yaba wa George da Acheampong, yana mai cewa “Na yi farin ciki da farko saboda makarantar horar da matasa ta Chelsea saboda shi (George) yana daya daga cikin yaranmu.”
Chelsea, wacce aka yi hasashen za ta lashe gasar Europa Conference League tun daga farkon kamfen din, na daf da tsallakewa zuwa zagaye na gaba bayan da ta doke Legia Warsaw. Idan suka tsallake, za su kara da Djurgardens na Sweden ko Rapid Vienna na Austria a wasan kusa da na karshe.