Yan Najeriya, musamman ‘yan siyasa da masu fafutuka, na ci gaba da cece-kuce kan tafiye-tafiyen da Shugaba Bola Tinubu ke yi zuwa ƙasashen waje ba tare da ya ba mataimakinsa, Kashim Shettima, riƙon gudanar da harkokin gwamnati ba.
Wannan cece-kuce ta ƙaru ne bayan tafiyar shugaban ƙasar ta “ziyarar aiki” ta mako biyu zuwa Faransa, inda fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa zai ci gaba da jagorantar harkokin gwamnati daga birnin Paris.
Masana tsarin mulki, ciki har da Barista Audu Bulama Bukarti, sun bayyana cewa sashe na 145 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi cewa dole ne shugaban ƙasa ya rubuta wa majalisar dokoki takarda don miƙa mulki ga mataimakinsa a matsayin riƙo idan zai yi tafiya.
“A gyaran da aka yi a 2010 aka yi amfani da kalmar Turanci ta ‘Shall’, wadda a tsarin doka take nufin ‘Tilas’,” in ji Barista Bukarti, yana mai jaddada cewa wannan tanadi ba zaɓi ba ne, dole ne a bi shi.
Lauyan ya kuma yi nuni da illar da aka fuskanta a baya lokacin da Marigayi Umaru Musa Yar’Adua ya tafi jinya ba tare da sanar da majalisar dokoki ba, wanda ya haifar da rikicin siyasa.
“Abin da shugaba Tinubu yake yi a yanzu biris ne da tanadin kundin tsarin mulki, ko kuma bai lura da wannan sashe ba,” in ji Bukarti, yana mai gargadin cewa za a iya fuskantar irin wannan matsala idan ba a bi doka ba.
Wannan cece-kuce ta haifar da tambayoyi game da bin doka da oda a gwamnatin Tinubu, kuma ‘yan Najeriya na ci gaba da kira ga shugaban ƙasar da ya bi tanadin kundin tsarin mulki.