Barcelona da Atletico Madrid na fafatawa kan ɗanwasan bayan Bournemouth, Marcos Senesi (28), wanda ya sanar da kulob ɗinsa zai bar su a 2026.
Manchester United na sa ido kan matashin ɗanwasan gaba Yan Diomande (19) daga Ivory Coast, yayin da RB Leipzig ke neman kusan fam miliyan 80 a kansa.
Har yanzu Man United ba ta fara tattaunawa da Atletico Madrid ba kan ɗanwasan tsakiya Conor Gallagher (25).
United za ta jinkirta sayar da Joshua Zirkzee saboda matsalar raunuka da kuma rashin ƴanwasan Afirka da suka tafi gasar nahiyar.
Liverpool na bibiyar ɗanwasan gaba na Brentford, Igor Thiago (24), domin ƙara ƙarfi a harin su.
Newcastle, Nottingham Forest da Crystal Palace na son ɗanwasan bayan Ajax, Youri Baas (22).
Arsenal na sha’awar matashin ɗanwasan bayan AC Milan, Davide Bartesaghi (19).
Bayern Munich na sa ido kan ɗanwasan Cardiff, Dylan Lawlor, wanda zai cika shekara 20 a Janairu.
Chelsea, Arsenal da Newcastle sun nuna sha’awa ga ɗanwasan tsakiya na Marseille, Darryl Bakola (18).