Bankin Duniya na shirin amincewa da rancen dala miliyan 500 ga Najeriya domin kara saukin samun kudi ga kananan ‘yan kasuwa Rancen zai gudana ta hannun bankin BDN na Najeriya, yayin da ‘yan kasuwa masu zaman kansu za su samar da mafi yawan kudin Shirin FINCLUDE zai taimaka wajen kirkirar sababbin hanyoyin bada bashi, rage hadari ga masu ba da rance, da habaka tsarin kudi.

Ana sa ran Bankin Duniya zai amince da rancen dala miliyan 500 ga Najeriya a yau Juma’a, a wani yunkuri na fadada damar samun kudi ga kanana da matsakaitan kamfanoni a fadin kasar. Rahotanni daga Bankin Duniya sun nuna cewa shirin da aka ware domin ‘yan kasuwa a Najeriya (FINCLUDE), zai jawo ra’ayin masu zuba jari tare da kirkirar sababbin hanyoyin tallafa wa ‘yan kasuwar.