Gwamnatin Amurka ta mayar wa Najeriya dala miliyan 52.88 da ta ce ta ƙwato daga tsohuwar ministar albarkatun man fetur ta ƙasar, Diezani Alison Madueke da wasu abokanta.
A ranar Juma’a ne Jakadan Amurka a Najeriya, Mr. Richard M. Mills, Jr, ne ya jagoranci tawagar da ta mayar da kuɗin zuwa ofishin ma’aikatar shari’ar ƙasar da ke Abuja.
Alsion-Madueke – wadda ra riƙe muƙamin ministar albarkatun man fetur a tsohuwar gwamnatin GoodLuck Jonathan daga 2010 zuwa 2015 – an zargeta da ɓarnatar da kuɗaɗen gwamnati masu yawan gaske, zargin da ta sha musantawa.
Haka kuma tana fuskatar shari’o’i masu alaƙa da cin hanci da rashawa a lokacin da take riƙe da muƙamin.
Amurka ta ce tsohuwar Ministar tare da abokanta sun sayi rukunin gidajen alfarma a biranen California da New York da kuma mallakar jirgin ruwa na alfarma a tsibirin Galactica Star.
Yayin da yake jawabi a wurin karɓar kuɗin, a madadin gwamnatin Najeriya, Ministan shari’ar ƙasar Lateef Fagbemi SAN ya ce mayar da kuɗin, wani muhimmin mataki ne a ƙoƙarin da gwamnatin ƙasar ke yi na yaƙi da cin hanci da rashawa.
A watan Nuwamban 2022 ma ƙasar ta mayar wa gwamnatin Najeriya dala miliyan 20.6 da ake zargin wani tsohon shugaban mulkin sojin ƙasar da sacewa.
BBC