Ambaliyar ruwa ta tilasta wa dubban mutane barin muhallansu a Maiduguri, babban birnin jihar Borno sakamakon fashewar madatsar ruwa ta Alau.
Rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama sun samu mafaka a waɗansu unguwannin da ambaliyar ba ta kai wurin ba bayan da madatsar ruwa ta Alau ta ɓalle, bayan cikar da ta yi tsawon mako ɗaya.
Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Farfesa Usman Tar ya fitar a safiyar Talata, ya yi kira ga mutane da su gaggauta tashi daga unguwannin da lamarin ya faru.
Ya ce “Sakamakon mamakon ruwan sama da ake samu a wannan shekara, muna kira ga mutanen da ke zaune kusa da koguna da su tashi nan take domin kare kansu da kuma dukiyoyinsu”.
Hukumomi a jihar ta Borno sun sanar da rufe dukkan makarantun jihar na tsawon makonni biyu.
Tituna da dama dai sun cika da ruwa wanda hakan ya janyo wahala wajen zirga-zirgar ababen hawa.
Bayanai sun ce lamarin ya fi muni a unguwannin Fori da Galtimari da Gwange da kuma Bulabulin.
Bidiyon da aka wallafa a shafukan sada zumunta na Facebook da X sun nuna yadda ambaliyar ta mamaye titunan Maiduguri a yayin da jama’a suka hau gadoji domin neman mafaka.
Ambaliyar ta shafi gidan adana namun daji, lamarin da ya sa dabbobi suka fita kan titunan suna gararamba.
Ambaliyar ita ce mafi muni a jihar Borno cikin shekaru 30